Ungategored

Ba zan zauna in zurawa Buhari ido ya ciwo bashin da zai lalatawa matasa rayuwarsu nan gaba ba – Atiku Abubakar

Ba zan zauna in zurawa Buhari ido ya ciwo bashin da zai lalatawa matasa rayuwarsu nan gaba ba – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019,Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai zauna yana kallo shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya batawa matasa gobensu ba

Atiku ya bayyana hakane a akan maganar bashin da gwamnatin shugaban kasa, muhammadu Buhari ke son ciyowa na dala Biliyan 29 wanda tun a zangon mulkinshi na farko ya so ya ciwo amma majalisar tarraya, karkashin jagorancin Bukola Saraki ta ki amincewa.

Saidai a yanzu kakakin majalisar, Ahmad Lawal ya bayyana cewa majalisar zata amincewa shugaban ya ciyo wannan bashi.

Atiku yace matsalar gwamnatinnan ba wai ciwo bashi bane koda ta ciwo bashin bata san yanda zata yi amfani dashi yanda ya kamata ba, yace shi da Obasanjo sun fitar da Najeriya daga kangin bashi a zamanin mulkinsu dan haka ba zai zauna yana kallon wannan gwamnati ta sake tsunduma Najeriya cikin bashin ba.

Yace bashin da Najeriya ke da shi yanzu haka yafi karfinta dan kuwa kudin da ake warewa na biyan bashi yafi wanda ake warewa dan ayyukan raya kasa yawa.

Yace a tsarinshi na gyaran tartalin arziki ya bayyana cewa zai yiwa kamfanin mai na kasa garambawul amma wasu da aka biya suka je suna bata mai suna wai yace zai sayarwa da abokanshi kamfanin, yace misali shine kamfanin mai na kasar Saudiyya wanda ya fi kowane kamfani samun riba a Duniya, ARAMCO wanda kwanannan aka sayar da hannun jarinshi kuma a karin farko ya kawo dala Biliyan 29, kudin da babu kamfanin da ya taba kawowa a Duniya.

Yace ba sai gwamnati ta ciwo bashi ba, zata iya bin irin waccan hanya da Saudiyya ta bi.

Atiku ya jawo hankulan matasa inda yace kada su yadda a musu wannan sagegeduwa su fito su yi magana, su gano su waye ke wakiltarsu a majlisu su rubuta musu wasikar cewa kada su yadda da maganar bashinnan.

Yace ba zai zauna ya kalli gwamnatin da bata da hangen nesa ba ta tsunduma Najeriya cikin matsala ba.

Back to top button
error: Content is protected !!