Labarai

Ya Rasu Bayan Kwana Biyu Da Daura Aurensa

Innalillahi Wa’inna ilaihi Raji’un! Ya Rasu Bayan Kwana Biyu Da Kara Aurensa A Garin SaminaKa.

Ya Gamu Da Ajalinsa Ne Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ta’aziyya A Garin Pambegua, Inda Yayi Hatsari Ya Hadu Da Ajalinsa, Mutumin Mai Suna Alhaji Kabiru, Ya Samu Saida Sosai A Wajen Al’umma Inda A Shaideshi Da Kirkinsa.

Tasiu Adam Abdullahi, Yayi Rubutu Game Da Mutuwar A Shafinsa Na Facebook Kamar Haka

Mutumin kirki ne me san jama a,daurin auren sa shekaran jiya asabar ya isa ka tabbatar da haka,jiya da magriba na ganshi da dan sa yake mana Godiya da ban gajiya amma yanzu mun yi bankwana dashi ya sadu da mahaliccin sa yan uwa, masoya makusanta da iyalan sa ga sabuwar amarya da tarewa ba aiba duk bai hana Allah gayyatar sa ba ya Allah ka gafarta masa kusakuran sa kasa aljanna makoma

DARUSSAN WANNAN RASHI

1. Ba Abin Da Ke Hana ajali Zuwa

2. Tayiwa Cikan Buri Yana Tare Da Ajali

3. Kayi Wa Mutuwa Tanadi Dan Bata Sanrwa

4. Arziki Ka Da Jama’arka Baza Su Hana Ka Mutuwa Ba Kada Ka Manta Lahira

5. Ka Zauna Da Kowa Lafiya Baka San Lokacin Mutuwa Ba

6. Mutwa wa’azi ce,amma jinsin wadanda a kai wa tafi duka matasa su kudi ku gina lahira ba gasar gidaje shaguna da plotai ba in ka mutu sai da a kirga su kawai amma ba za ka tafi da komai ba

A karshe muna addu ar Allah ya gafarta masa da sauran musulmi baki daya

 

Back to top button
error: Content is protected !!