Ba Kawai rawa Da Waka Ne ke Da Muhimmanci A Fim Ba – ZPreety
Zulaihat Ibraheem jaruma ce da aka fi sani da ZPreety bata dade da shigowa masana’antar Kannywood ba amma ta samu daukaka mai tarin yawa
An haifeta ne a 1997 kuma ‘yar asalin jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba dake karamar hukumar Dankuwa
Jarumar ta bayyana cewa, ta shigo harkar fim amma hankalinta na kan aure, a duk lokacin da ta samu miji zata bar fim ta yi aurenta
Zulaihat Ibraheem jaruma ce da aka fi sani da ZPreety. Jaruma ce da bata dade da shigowa masana’antar Kannywood ba amma ta samu daukaka mai tarin yawa. Ba a fim kadai ta tsaya ba, ta kasance tana yin gajerun bidiyon ban dariya inda take wallafa su a shafinta na Instagram. Hakan kuwa ya sa tayi farin jini da karin suna.
Kamar yadda jarumar ta bayyanawa jaridar Fim Magazine, an haifeta ne a 1997 kuma ‘yar asalin jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba dake karamar hukumar Dankuwa. Don haka asalin iyayenta Dakarkari ne a yankin Zuru.
Kamar yadda ta bayyana, tayi karatun firamare a barikin sojoji na jihar Legas saboda mahaifinta ma’aikacin hukumar kula da shige da fice ne wato Nigerian Immigration Service. Ta yi sakandire a Kontagora a jihar Neja. Tayi karatu a kwalejin horar da malamai ta tarayya da ke Sokoto amma a halin yanzu tana jami’ar ABU Zaria inda ta ke matakin kusa da na karshe na kammala digirinta na farko.