Kannywood

Ba Duka Yan Fim Bane Suka Taru Su Zama Daya

Wata sabuwar yar wasa a masana’antar shirya fina-finan Hausa, Khadija Alhaji Shehu wacce aka fi sani da Khadija Yobe ta yi kira ga mutane da su guji yi wa yan fim kudin goro har su dauka cewar duk halinsu iri guda idan wani ya yi ba daidai ba a cikinsu.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da majiyarmu ta Mujallar Fim.

Ita dai Khadija Yobe, ana yi mata ganin ta shigo harkar fim da kafar dama domin kuwa duk da yake ba ta dade a ciki ba, amma ta samu shiga cikin manyan fina-finai da dama.

Hakan ya nuna cewar ita ma nan gaba kaɗan za ta iya shiga cikin sahun manyan jaruman da ake damawa da su.

Ba abin mamaki ba ne idan har hakan ta kasance, domin kuwa da ilimin ta Khadija ta shigo Kannywood. Ta na da digiri a fannin gudanarwa, wato ‘Public Administration’. Don haka ana hangen ko me za ta yi sai ta auna shi.

A hirar ta da aka yi da ita jarumar ta bayyana cewa ita asali Bafillatana ce daga garin Damaturu a Jihar Yobe. Amma haifaffiyar Maiduguri ce a Jihar Borno. Sai dai duk karatun ta a Damaturu ta yi shi.

Da aka tambaye ta yadda aka yi ta samu kan ta a Kano kuma har ta shiga masana’antar finafinan Hausa, sai Khadija ta amsa: “To gaskiya garin Kano ni ba baƙuwa ba ce, domin lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani sai baban mu ya taso, mu ka dawo Kano. Sai da mu ka yi shekara huɗu, mu ka koma gida.

“To kuma da man mu na da ‘yan’uwa da yawa a nan, don haka ko da na gama karatu na, na ji ina son na shiga harkar fim, sai na dawo na zauna a wajen ‘yan’uwan mu.

“Don haka yanzu ina garin Kano da zama.

“Na zo masana’antar Kannywood ne domin ni ma na bada tawa gudunmawar, domin tun ina yarinya na ke so na yi fim, sai dai a lokacin ban samu dama ba.”

Back to top button
error: Content is protected !!