Ba Daidai Ba Ne Malaman Addini Su Dinga Yi Wa Siyasar Dimokraɗiyya Katsalandan
Ba Daidai Ba Ne Malaman Addini Su Dinga Yi Wa Siyasar Dimokraɗiyya Katsalandan-Cewar Matashin Ɗangwagwarmaya Auwal Shu’aibu
Auwal Shu’aibu ya ce lokacin da mutanen kudu ke fafutakar zanga zangar kawo ƙarshen ‘yan sandan SARS da ke addabarsu, ƙungiyar CAN da sauran maluman addinansu basu ya masu katsalandan ba, haka zai yi wuya kaga ƙungiyar CAN ta shiga sabgar da ba tata ba, amma wasu Maluman Addini a Arewa sun mayar da kansu ‘yan kanzagin ‘yan siyasa, waɗanda ‘yan siyasa ke amfani da su wajen cimma manufofinsu.
“Ita siyasar dimokuraɗiyyar tana da irin nata tsarin, don haka ba daidai ne Malamai sun dinga yiwa dimokuraɗiyyar karan tsaye ko katsalandan ba, idan ko suna sha’awar yin haka, kamata yayi su shiga siyasa, kada suyi haka da rigar Malumta” inji matashin ɗan gwagwarmayar.