Ba Abu Mai Kyah Bane Ya Raba Adam A Zango Da Ummi Rahab
Datti Assalafy Ya Bayyana Cewa Ba Abu Mai Dadi Bane Ya Raba Adam A Zango Da Ummi Rahab, Inda Ya Shaida Cewa A Binciken Da Yayi Ya Gano Cewa Mahaifiyar Ummi Rahab Ta Damkama Adam A Zango Yarinyarta Ne Tun Yarinyar Tana ‘Yar Karama Bata Balaga Ba.
Ga Bidiyon Barazar Da Ummi Rahab Din Ta Ma Adam A Zango Akan Zata Tona Mishi Asiri Idan Yaci Gaba Da Magana Akanta
Ga Abin Da Hake Cewa
Kamar yadda aka saba Datti Assalafiy ya gudanar da bincike, kuma na samu tabbacin cewa tabbas Adam Zango ya rabu da Rahab, kuma rabuwar banza sukayi, rabuwar uwaka ubanka, na kuma samu bayani akan abinda ya rabasu har ita Rahab tayi barazanan tona masa asiri bayan BBC Hausa sunyi hira da Adam Zango a jiya Alhamis inda ya fadi wata kalma
Na fahimci cewa hakika mahaifiyar Ummi Rahab (Allah Ya jikanta) tayi babban kuskure da ta dauki amanar ‘yarta ta damkashi a hannun wanda shima yana bukatar a bashi tarbiyyah
Gaskiya wannan rayuwa rikon amana tayi karanci, cin amana ya yawaita, ba kowa ake bawa amana ba, wadanda ake ganin suna da tsoron Allah a wannan zamanin suna iya cin amana, balle ‘yan daudu masu lalata tarbiyyan al’ummah
Malaman tarbiyya Islama sunce, ko halal ce akwai wata halal din da ana barinta don kunya, balle abinda bai halalta ba
Shawaran da zan bamu shine:
Duk wanda Allah Ya bashi mata da ‘ya’ya musamman mata, to yayi kokarin basu tarbiyya ta addini, a wannan zamanin ba’a bada amanar mata, walau matarka na aure ko ‘yarka da ka haifa, idan suka samu tarbiyya da juriya suna sana’a ko mutuwa kayi zasu kubuta da taimakon Allah
Allah Ka tsare al’ummar Musulmin Kasar Hausa daga sharrin ‘yan Hausa film Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum