AVANGER: Sabon Fim Din Turanci Da Ya Zo Da Sabon Salo A Masa’antar Finafinan Hausa
AVANGER: Sabon Fim Din Turanci Da Ya Zo Da Sabon Salo A Masa’antar Finafinan Hausa
…an kashe masa sama da milyan goma
…ya tara fitattun jarumai maza da mata
Shahararren kamfanin shirya finafinan Hausan nan, mai suna M.M Haruna Films Production Nig. Ltd, wadanda suka shirya finafinai irin su ‘Hangen Nesa’, ‘Husna Ko Huzna’ a yanzu ya shirya kawo gagarumin sauyi a masana’antar fim din Hausa, inda za su shirya wani kayataccen fim din Turanci mai dauke da darrusa wanda ake ganin ba a taba shirya fim makamancin sa ba a masana’antar Kannywood.
Fim din mai suna ‘Avenger’, yana dauke da manyan fitattun jaruman Kannywood, manyan ma’aikatan fim, sannan ya samu kayan aiki na zamani.
Haka kuma fim din an ware masa kudi sama da milyan goma domin daukarsa. Don gamsar da masu kallo.
Tuni dai aka soma daukar shirin fim din, wanda yake dauke da jarumai irin su Ali Nuhu, Abba Elmustapha, Shu’aibu Lawan Kumurci, Sani Mu’azu, Rahma Sadau, M.M Haruna, Mustapha Musty, Hussaini Sule Koki, Shamsu Dan Iya, Iliyasu Abdulmumin Tantiri da sauransu.
M.M Haruna shi ya kawo labarin fim din, Ibrahim Birniwa kuma ya tsara shi, mashiryan shirin kuma sun hada da Usman Mu’azu da Nazifi Asnanic.
Bature Zambuk shi ya bada umarnin fim din, inda Yunusa Mu’azu ya taimaka masa.