Auren wuri yana kare cutar karin mahaifa-Likitoci
Auren wuri yana kare cutar karin mahaifa-Likitoci
Likitoci a bangaren haihuwa sun bayyana cewar auren wuri yana hana kamuwa da ciwon karin mahaifa.
Wani babban mata a birnin Ikko Dakta Gabriel Akilo ke bayyana hakan a wajen wani taron karawa juna sani karo na 9 daya gudana a jihar Legas ranar Alhamis data gabata.
Dakta Akilo yace cutar tana kama mata ne lokacin da shekarun su suka tura batare da haihuwa akai akai zamanin budurci ba.
Likitan yace binciken su ya gano cewar auren wuri, da kuma haihuwa a lokutan kuruciya yana karawa mahaifa lafiya, idan kuma girma ya fara kama su kuwa akwai bukatar su huta, a cewar sa.
Akwai bukatar mu tattauna wannan babbar matsala dake fantsama kamar wutar daji, ciwon na karin mahaifa yana yawaita a tsakanin mata ne yan shekaru 35 zuwa 45.
Ko da yake likitan yace zai yi wuya a samu yan kasa da shekaru 20 da wannan lalura, a saboda haka yake shawartar mata su rungumi auren wuri domin samun lafiyar jiki data ciki domin kawar da cutar a kasarnan.
A ganin sa ba wani abune ke hana matan auren na wuri ba illa ruwan ido, da yace anan ne suke jifan gafiyar bedu wajen asarar maza nagari.
Dakta Akilo ya bukaci iyaye su karfafawa yayan su mata gwiwar auren wuri domin kawar da lalurar karin mahaifa a tsakanin al’umma.
Daga nan likitan ya ja hankalin mata game da magunguna da suke sha domin samun saukin cutar, gudun kaucewa rasa idanu a wajen neman gira.
Yace wasu magungunan su kan illata koda, mafitsara, yayan hanji da dukkanin bangarori dake taimakawa kwaryar ciki.