Ashe Abin Da Yasa Tahir Fagge Rawan Gala Kenan
Allah SarKi! Abin Tausayi. Tahir Fagge Yayi Cikakken Bayanin Dalilin Da Yasa Yake Rawa Da Yan Mata A Gidan Gala, Fitaccen Jarumin Na KannyWood Ya Bayyana Cewa Kowa Da Irin Kaddararsa A Rayuwa. Inda Yace Yanzun Mutane Basa Yadda Da Kaddara.
Jarumin Yayi Bayyani Ne A Hirar Da Akayi Dashi A Shashen BBCHausa, Cikin Shirin Nan Na Daga Bakin Mai Ita. Tahir Faggen Yace Ya Fara Zuwa Gidan Gala Yana Rawa Da Yan Mata Ne Sanadiyyar Neman Kudin Jinyar Rashin Lafiyar Ciwon Zuciya Da Yake Fama Dashi.
Ya Bayyana Cewa Ya Dade Yana Fama Da Ciwon Zuciya, Inda Har Yanzun Yake Fama Da Ciwon Na Zuciya, Wanda Hakan Ke Sashi Neman Kudin Magani Idan Maganinsa Ya Kare.
Sanadiyyar Ciwon Zuciyar Da Yake Fama Dashi Me, Sai Wasu Dasu Bude Sabon Gidan Rawa Na Gala Su Gayyaceshi Domin Yazo Ya Zama Babban Bako Da Za.a Bude Gidan Dashi. Inda Bayan Sun Gama Raye Rayen Nasu Ne, Sai Suka Bashi Kudi Sama Da Naira Dubu Dari, Hakan Yasa Ya Hada Da Sauran Kudaden Dake Hannunsa Yayiwa Kansa Maganin Ciwon Zuciyar Da Yake Fama Dashi
Tahir Faggen Yayi Cikakken Bayani Game Da Dalilan Da Susa Ya Taba 6acewa Daga Masana’antar KannyWood Din, Ya Kuma Bayyana Yadda Har Ya Fara Fitowa A Cikin Fina Finan Na KannyWood.
Ga Cikakken Bidiyon Yadda Jarumin Ke Bayani Dalla Dalla.