Kannywood

An Zabi Sabbin Shugabanni A Kannywood

Kungiyar Masu Shirya Fina-finai na Arewa ta Najeriya ‘The Arewa Film Makers Association of Nigeria’, AFMAN ta kammala zaben sabbin shugabanin ta.

An gudanar da zaben cikin zaman lafiya da lumana a ranar Asabar 17 ga watan Augusta a garin Kano kuma an mika wa wadanda su kayi nasarar takardun shaida wato satifiket.

Anyi takarar kujeru daban-daban kuma daga karshe an samu wadanda suka lashe zaben.

Tsaffin jaruman Kannywood wanda kuma suna cikin kwamitin amintattun na kungiyan ne suka gudanar da zaben a Kano.

A yayin da ya ke sanar da sakamakon zaben, Shugaban kwamitin zaben, Salisu Mohammed ya ce anyi adalci yayin gudanar da zaben.

“Munyi zabe cikin adalci da aminci kuma an samu wadanda suka yi nasara. Dukkan wadanda su kayi nasara a zaben da su rike mukammai a kungiyar daga yanzun zuwa shekarar 2021 kafin a sake zaben sabbin shugabanni.” inji Mohammed.

Ga jerin sunayen wadanda suka yi nasara da mukamansu:

1. Jamilu Yakasai – Shugaban AFMAN

2. Lawal Ahmed – Mataimakin Shugaba

3. Abdullahi Habibu – Audita

4. Aminu Dambazau – Mataimakin Sakatare

5. Rabiu The King – Sakataren Tsare-tsare

6. Abubakar Gboy – PRO

7. Halima Ateteh – Mai kula da walwala

8. Hannatu Bashir – Sakataren Kudi

Back to top button
error: Content is protected !!