An Yankewa Wanda Ya K@she Ummita Hukunci
Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Geng Quarong hukuncin kis@ ta hanyar rataya saboda k@she budurwarsa, Ummukhulsum Sani Buhari.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Haruna Dederi ne ya tabbatar wa BBC hukuncin kotun bayan zaman shari’ar da aka yi ranar Talata.
Ya ce “alƙali ya yi hukunci inda ya sami Frank da laifin kis@n kai wanda hukuncinsa kis@ ne kuma ya zartar da hukunci a kan haka.” in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa “ita shari’a tana da farko tana da ƙ@rshe, kuma abubuwan da aka iya bi sawu aka gano yayin tuhumar wanda ake tuhuma sune ake kafa hujja da su a kai ga hukunci,”
“Abubuwan da suka gabata sune suka wajabta wa kotu ta ɗauki irin wannan matsayi.” kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
A ranar 16 ga Satumban 2022 ne ɗanChinan ya daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.