Kannywood
An tafkawa Hadiza Gabon Sata Kuma Ta Yi Allah Ya Isa
Tauraruwar fina-finan Hausa,Hadiza Gabon ta bayyana cewa satar da daya daga cikin bankunan kasarnan ke mata ta yi yawa.Hadizar ta bayyana hakane
a shafinta na sada zumunta inda ta saka hoton kudi, Naira 700 da bakin access suka cire mata.
Ta yiwa goton taken “Satar Naku sai Karuwa Yake”
“Me yasa?”
“Nikam Allah ya Isa Kamar kudinku”
Saidai wani ya bata shawarar cewa ta kira masu kula da hulda da kwastomomin bankin amma tace ko ta kira basa dauka.