Kannywood

An Sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an yi sulhu a tsakanin manyan fitattun jaruman nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a garin Kano, bayan gumurzun da suka tafka.

Hadakar kungiyar nan ta masu shirya fina-finan Hausa ta kasa wacce aka fi sani da MOPPAN karkashin jagorancin Abdullahi Maikano ce ta yi nasarar shirya jaruman biyu.
Anyi hakan ne a ofishin jigon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar, 13 ga watan Afrilu.

Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu a kotu.

Back to top button
error: Content is protected !!