Labarai

An Sha ‘Zagin’ Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba

Fitaccen malamin addinin musulunci, Ahmed Gumi, ya ce wadanda ba musulmi ba sun sha zagin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a lokacin da ya ke raye, amma bai taba kowa ba ko kashe masu yi masa batanci.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani zaman karatu da ya yi a masallacin Juma’a a Kaduna, rahoton Premium Times.

Annabi kai kashe munafikai da ke zaginsa ba a lokacin da ya ke da rai, Gumi 

Malamin, kamar yadda ya furta a wata bidiyo da Ahmad Bulama ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce manzon Allah bai yi ramuwa ko kashe wadanda suke cutar da shi da zaginsa ba don kada a rika yayatawa cewa Annabi na kashe abokansa.

Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana kan kashe daliba kirista yar makarantar Shehu Shagari ta Ilimi a Sokoto kan zarginta da furta kalaman batanci ga Manzon Allah.

Ya bayyana cewa hanyar da ta fi dacewa musulmi su nuna kaunarsu ga Annabi Muhammad (SAW) shine bin koyarwarsa sau da kafa a maimakon kashe mutane kan wasu abubuwa.

Duk wanda ya kashe wanda suka yi alkawarin zaman lafiya tare bai zai ji kanshin aljanna ba nisanta shekarar 40,

A cewarsa, musulmi da kirista sun amince su zauna a kasa daya, don haka Najeriya kasa ce da ake hukunci da kundin tsarin mulki ba shari’a ba.

Don haka, duk wanda ya kashe wani da ba musulmi ba da suka yi alkawarin zama lafiya, ba zai ji kamshin aljanna nisanta shekara 40 ba,” in ji shi.

Gumi, yayin da ya ke cewa babu wanda aka bawa dama a dauki doka a hannunsa a musulunci, ya yi kira ga malaman addinin musulunci su rika koyar da mabiyansu ilimi mai nagarta a maimakon tunzura su aikata ‘munanan’ ayyuka.

Idan muna tunanin kashe Deborah, zai sa mutanen ba ba musulmi ba su dena zagin annabin mu, ya nuna muna mafarki ne,” ya ce.

Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

A wani rahoton, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Asalin Labari Daga Hausa Legits

Back to top button
error: Content is protected !!