Labarai

An Kwantar Da Daso A Gadon Asibiti

Sharrin Delegate’s: An kwantar da Yar Takarar Sanata Hajiya Saratu Gidado Wacce Akafi Sani Da (Daso) A Gadon Asibiti Bayan Abin Da Delegates Suyi Mata. Jaridar Jekadiyar Zamfara Ne Ta Ruwaito Labarin Tare Da Wallafa Wani Bidiyo Na Hajiya Dason A Gadon Asibiti.

Idan Baku Manta Ba, Kwanakin Baya Ne Dai Hajiya Saratu Gidadon Ta Fito Ta Bayyana Cewa Delegate Sunci Kudinta Amma Kuma Sunki Zabenta, Don Haka Dole Su Dawo Su Bata Kudinta, Sai Dai Hajiya Dason Tace Ta Daga Musu Kafa Kafin Wani Lokaci. Domin Su Sami Damar Dawo Mata Da Kudinta.

In Kuma Ba Haka Ba Sai Dai Su Hadu A Kotu, Domin Nan Ne Za.a Kwatar Mata ‘Yancinta. Ta Kara Da Cewa Bataci Nanin Ba, Nanin Bai Kamata Yacita Ba.

Sai Dai Har Zuwa Yanzun Babu Sunan Jam’iyyar Da Dason Ta Fito Takara, Don Haka Kawai Mun Dauki Wannan Lamarin Nata Ne A Matsayin BarKwanci. Tayi Ne Kawai Domin Bawa Mabiyanta Na Shafukan Sada Zumunta Nishadi.

https://youtu.be/8_dMwt7BuyI

Back to top button
error: Content is protected !!