Labarai

An kama shinkafar kasar waje a gidan ‘ma’ajin’ shugaba Buhari a Daura

Jami’an hukumar hana fasa kwabri da aka fi kira da ‘Kwastam’ dake aikin atisayen hana fatauci a kan iyakar Najeriya da kasar Nijar sun kwace buhunhunan shinkafar kasar waje 140 da suka samu a wani gidan ajiya mallakar Alhaji Habu Sarkin Fulani, makusanci kuma yardajjen shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Sarkin Fulani aminataccen shugaban kasa ne dake karba tare da adana duk kayan da aka kawo wa Buhari a matsayin kyauta.

Daily Nigerian ta wallafa cewa jami’an Kwastam sun kai samame gidan ajiyar dake unguwar Fegi a garin Daura bayan samun bayanan sirri.

A cewar jaridar, majiyarta ta sanar da ita cewa an bayar da kyautar buhunhunan shinkafar ne ga shugaba Buhari kafin a saka dokar hana shigo da shinkafar kasashen ketare.

Alhaji Sarkin Fulani amintaccen shugaba Buhari ne. Mutum ne mai amana da ba ya taba duk abin da aka bashi ajiya ko kuma ba nasa ba, koda kuwa wannan abun zai lalace.

Shine yake ajiye wa shugaban kasa kaya masu yawa a gidan ajiyarsa dake Fegi a Daura. Shine yake kula da shanu da gonar Buhari a Daura.”
“Yana zama tare da Buhari, duk lokacin da ya ziyarci Daura, tare da yi masa bayani a kan dukkan kayan da aka kawo masa kyauta, sannan shi kuma shugaba kasa zai sanar da shi yadda za a kasafta ko amfani da kayan ,” a cewar majiyar Daily Nigerian.

Daily Nigerian ta ce ta tuntubi kakakin rundunar hukumar Kwastam, Joseph Attah, amma kuma bai amsa kiran wakilinta ko mayar da amsar sakon da ya aika masa ba domin neman jin ta bakin hukumar kwastam a kan lamarin.

Tun bayan da aka ska dokar haramta shigo da shinkafar waje Najeriya, jami’an hukumar suke kai samame kasuwanni da gidajen ajiya domin farautar shinkafar waje da ake shigo wa da ita ta barauniyar hanya.

Back to top button
error: Content is protected !!