An Gano Yadda Takardar Shaidar Karatun Atiku Ke Ɗauke Da Sunan Sadiq Abubakar
ALLURA ZATA TONO GALMA: An Gano Yadda Takardar Shaidar Karatun Atiku Ke Ɗauke Da Sunan Sadiq Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fito ya bayyana dalilin da yasa satifiket ɗin sa na jarabawar kammala sakandare (SSCE) ke dauke da suna daban, Sadiq Abubakar, maimakon Atiku Abubakar.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya yi wannan ƙarin haske ta bakin Dele Momodu a shafinsa na X.
Momodu wanda shine Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, ya ce wannan bayanin wani martani ne ga zarge-zargen da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki suka yi wa shugaban nasa.
Ya yi iƙirarin cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi tambaya kan sunan ‘Sadiq Abubakar’ a cikin takardar shaidar kammala jarabawar WAEC ta Atiku saɓanin sauran takardun sa.
Momodu, ya ce ya mika tambayoyin ga Atiku, wanda ya bayar da amsar saɓanin da aka samu.







