Labarai
An Cigaba Da Shirya Addu’ar Alƙunutu A Mazaɓar Gama A Jihar Kano
An Cigaba Da Shirya Addu’ar Alƙunutu A Mazaɓar Gama A Jihar Kano.
Mazaɓar Gama tayi fice ne sunanta ya fito fili a ɗaukacin Kano dama Najeriya a shekarar da aka yi ‘Inkwakulusib’ a zaɓen jihar Kano, lokacin da tsohon gwamnan Kano Umar Ganduje yayi nasara kan gwamna mai ci a yanzu wanda wanda da farko ake yi wa kalon samun nasara amma reshe ya juye da mujiya.
Tun a wannan lokaci na Inkwalkulusib garin Gama yayi fice, sai dai a yanzu ma a wannan lokaci ga duk alamu mutanen garin na ƙoƙarin sake fito da sunan garin ta fuskar addu’ar Alƙunutu.