Kannywood

An Ɗaura Auren Fatima ‘Yar Ado Gidan Dabino

A RANAR Asabar, 2 ga Satumba, 2023 aka ɗaura auren ɗiyar fitaccen marubuci kuma jarumi, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, wato Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino, da angon ta, Bello Umar Kawaji.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11 na safe a Masallacin Juma’a na Al-Furƙan da ke unguwar Nassarawa GRA, Kano, a kan sadaki N100,000, kuma an biya lakadan kuma wakilin waliyyin amarya, Alaramma Muttaƙa Sani ya karɓa.

Uban amarya (na 2 daga hagu) tare da jama’a a wajen ɗaurin auren

Wakilin mujallar Fim ya ruwaito cewa taron ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane kama daga sarakuna da marubuta da kuma ‘yan siyasa.

Waɗanda su ka halarta sun haɗa da Farfesa Abdalla Uba Adamu, Farfesa Yusuf Adamu, Dakta Tahir A. Ahmad Sarkin Dawaki Maituta, Kabiru Assada, Aminu Ladan Abubakar (Ala Waƙa), Zaharaddin Ibrahim Kallah, Mai Unguwar Mandawari Alhaji Ibrahim Muhammad Madawari, da Khadil Imam.

Ado Gidan Dabino tare da Farfesa Yusuf Adamu (a damar sa) da Aminu Alan Waƙa (a hagun sa) da sauran jama’a

Tun kafin ranar ɗaurin auren an shirya wa amarya Fatima taron saukar karatun Alƙur’ani da addu’o’i, sannan bayan an ɗaura da yammacin ranar Asabar ɗin an yi taron addu’a na musamman a gidan Ado Ahmad Gidan Dabino domin Allah ya kawo zaman lafiya a tsakanin ango da amarya kuma ya tsare su daga dukkan fitintinu na zaman aure.

Allah ya tabbatar da hakan, amin.

Farfesa Abdalla a tsakiyar mahalartan ɗaurin auren
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino tare da Kabir Assada (mai farar babbar riga) da sauran mahalarta ɗaurin auren Fatima
Amarya da ‘yan’uwa da ƙawaye a wajen taron addu’ar musamman
Amarya da sauran mata su na karatun Alƙur’ani
Ado Gidan Dabino da iyalin sa a lokacin addu’ar musamman da aka yi a gidan sa

 

Back to top button