Kannywood

Amal Umar zata yi Aure a wannan watan – Mujallar Fim

FITACCIYAR jaruma Amal Umar za ta yi aure a ƙarshen wannan wata na Janairu, 2020, wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim.


Majiyar, wadda ke kusa da jarumar, ta tabbatar mana da cewa duk wani shiri na bikin ya kammala.


“An fitar da ranar 27 ne za a ɗaura auren na Amal tare da wani saurayin ta da ta daɗe ta na soyayya da shi,” inji majiyar.
Majiyar, wadda ta buƙaci a sakaya sunan ta, ta tabbatar wa da mujallar cewa Amal ta na ɓoye maganar bikin nata ne har sai ya rage kwanaki kaɗan sannan duniya ta sani.


“Amma dai duk wani shiri na bikin ya riga ya kammala, don haka lokaci kawai ake jira,” inji majiyar.
Binciken mujallar ya gano cewa wani fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa ne jarumar za ta aura.


Sun daɗe su na soyayya da shi, don haka ga duk wanda ya san alaƙar su, to yin aure a tsakanin su ba wani abin mamaki ba ne.
Da yake Amal ta na nuƙu-nuƙu da maganar auren nata, ƙoƙarin mujallar Fim ta yi magana da ita a kan maganar ya ci tura.


Wakilin mujallar ya kikkira ta amma ya na samun wayar a kashe, kuma ba ta bada amsar tes da ya tura mata ba kafin rubuta wannan labarin.
Kwanan nan ne dai jarumar ta dawo daga aikin umrah.


Ta na daga cikin ƙananan ‘yanmata da su ka shigo harkar fim da ƙafar dama, domin cikin ƙanƙanen lokaci ta fito a manyan finafinai da su ka ɗaga sunan ta.
Kuma da yake ta iya Turanci, an saka ta a wasu manyan finafinan kudancin Nijeriya, na Nollywood.

Back to top button
error: Content is protected !!