Kannywood

Amal Umar Ta Zama Ta Farko Da Zata Fara Aure A Kannywood A Wannan Shekarar

Wata majiya kwakwara ta tabbatar da cewa matashiyar jaruma Amal Umar, zata zama amarya a ranar 27 ga watan Janairu.

Wata majiya kwakwara ta tabbatar da cewa matashiyar jaruma Amal Umar, zata zama amarya a ranar 27 ga watan Janairu

Majiyar ta tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye da ya danganci bikin auren jarumar ya kammala amma ta boye ne har sai ana gab ta sanar

Kamar yadda bincike ya nuna, jarumar zata auri wani fitaccen dan kwallon kafa ne don sun dade suna soyayya dashi

Sananniya kuma fitacciyar matashiyar jaruma, Amal Umar za ta yi aure a wannan watan na Janairu 2020, in ji wata kwakwarar majiya da ta sanar wa mujallar Fim.

Majiyar, wadda ke da kusanci da jarumar, ta tabbatar mana da cewa duk wani shiri na bikin ya kammala.

“An fitar da ranar 27 ga watan janairu don daura auren Amal tare da wani saurayi da ta dade tana soyayya dashi,” cewar majiyar.

Majiyar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa Amal ta na boye maganar bikin nata ne har sai ya rage kwanaki kadan sannan duniya ta sani.

Binciken mujallar Fim din ya gano cewa, matashiyar jarumar zata auri wani fitaccen dan kwallon kafa ne. Sun dade suna soyayya da shi, don haka ga duk wanda ya san alakarsu, to yin aurensu ba wani abun mamaki bane.

Back to top button
error: Content is protected !!