Labarai

Allah Yama Sarkin Zazzau Shehu Idris Rasuwa

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa.

 

Ya rasu ranar Lahadi.

Uban Garin Zazzau kuma Hakimin Soba, Alhaji Bashir Shehu Idris wanda ɗa ne ga marigayin shi ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

 

Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

 

Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84, bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

 

Tuni Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya wallafa saƙon ta’aziyyarsa a shafinsa na Twitter, inda gwamnan ya ce za a yi jana’izar Sarkin a Fadar Zazzau a yau Lahadi da misalin ƙarfe biyar na yamma.

 

Kauce wa Twitter, 1

 

Daga BBCHausa

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button