Kannywood

Ali Nuhu Ya Maka Adam A Zango A Kotu, Duba Takardan Sammaci

Fittacen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya yi karar Adam A Zango a kotu kan cewa kotu ta shiga tsakaninsa da Zango kuma ya daina ba ta masa suna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na dauke ne cikin takardan kirar kara wanda Ali Nuhu ya shigar a kotun USC da ke Fagge a Kano.
Kotun ta bukaci Adam Zango ya gurfana gaban a ranar 15 ga watan Maris na 2019 misalin karfe 8.30.
“Kotu tana kiran ka a kan shari’a da ke a gabanta na neman shiga tsakani a kan bata suna don haka sai ka zo kotu ranar da na ambata a sama,” kamar yadda aka rubuta a jikin takardan sammacin.
Back to top button
error: Content is protected !!