Kannywood

Ali Nuhu Ya Cika Shekaru 20 A Masana’antar KannyWood

Jarumin jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim
Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999
Tauraronsa na ci gaba da haskawa a masana’antar duk da tsawon shekarun nan da ya dauka yana harkar
Shahararren jarumin nan da yaga jiya yaga yau a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya cika shekaru 20 da fara harkar fim.
Ali Nuhu dai ya shiga masana’antar shirya fina-finai a sa’a cikin shekarar 1999.
Jarumin ya samu tarin nasarori kama daga lambar yabo da dama, da kuma tarin daukaka bama a arewacin kasar kawai ba, harma ga sauran sassan kasar dama duniya baki daya.
Tun a zamanin da ya fara fitowa a wasanni tauraronsa ke haskawa inda aka yi ittifakan babu wanda ya kais hi farin jini a masana’antar gabaki daya kama daga wadanda suka fara harkar tare har zuwa ga wadanda ke tasowa a yanzu.
Hakan ya sanya ake yi masa inkiya da sarki mai Kannywood. Sai dai hasashe sun nuna cewa sirrin daukakarsa na daga hazaka da kokarin jarumin akan sana’arsa, sannan kuma shi din mutum ne mai son ganin ci gaban wadanda ke tasowa a masana’antar.
Ya kuma zamo silar shigowar mutane da dama masana’antar, sannan kuma ya zamo silar daukakarsu. Cikin irin wadanna mutane da ya kawo akwai Rahama Sadau wacce tauraronta ke haskawa, da kuma Maryam Yahaya da dai sauransu.
Muna taya jarumin murnar wannan tafiya mai nisa da yayi a rayuwarsa!
Back to top button
error: Content is protected !!