Kannywood

Ali Nuhu Ya Cancanci Matsayi A Gwamnati, Ko Ba Alfarma

Ali Nuhu

A DUk muƙaman da Ministar Fasaha, Al’adu Da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Barista Hannatu Musa Musawa, ta ba ‘yan Arewa a ma’aikatar ta, ban ga wanda ya cancanta sama da na Ali Nuhu ba. Ban kuma ga wanda ‘yan Arewa za su amfana da shi sama da nasa ba.

Ba bambaɗanci na ke masa ba. Don ba mu da wata alaƙa da shi a yanzu. In ya gan ni ma ba lallai ne ya gane ni ba. Sanayya ta da shi tun ta 1998 zuwa 2002 ce lokacin da daraktan daraktoci Tijjani Ibrahim ya kwanta dama. Sai alaƙar ganin juna ta yanke tsakani na da shi. Amma kafin lokacin kusan kullum mu na haɗuwa da shi a gidan marigayin.

Sarki Ali Nuhu tun a wancan lokacin mutum ne mai jajircewa a kan abinda ya sanya a gaba. Ba ya wasa. Ya na da biyayya. Daga baya kuma ya zama mutum wanda ba ya son raini.

Kaf a ‘yan fim babu wanda ya dace da wannan muƙamin sama da Ali Nuhu. Don haka a lokacin da na ji labarin an ba shi muƙamin Manajan-Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) na cika da murna da addu’ar Allah ya ba shi wuyan ɗauka.

Ali mutum ne wanda yake da son cigaban duk wanda alaƙa ta haɗa shi da shi ta mutunci. In dai jinin ku ya haɗu da shi, to tabbas zai maka komai wanda zai ga ya cicciɓa ka zuwa ga samun nasara.

Shi kaɗai ne a Kannywood ya cicciɓa mutane da yawa wanda a zuciyar sa babu wata hiyana ko tunanin za su zo su fi shi bare ya yi musu gori.

Kaɗan daga cikin mutanen da ya cicciɓa taurarin su sukai haske a Kannywood sun haɗa da marigayi Ahmad S. Nuhu, Adam A. Zango, Auwal Isa (West), Lawan Ahmad, Sadiq Sani Sadiq, Sadiq Ahmad Jos, Shamsu Ɗan’iya, Safiya Musa, Hafsat Shehu da Zainab Idris

Akwai kuma Fati Abubakar (Karishma), Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Maryam Yahya, Teema Makamashi, Maijidda Ibrahim (Khusufi) da sauran ɗimbin jarumai maza da mata, yara da manya. Wasu ba zan iya kawo sunayen su ba.

Akwai marubuta ma da ya haska su ko ya cicciɓa darajar su. Kaɗan daga cikin su akwai irin su Ibrahim Birniwa, Jamil Jiddan Nafseen, Mujahid S. Koguna, Abdulkarim Papalaje, da sauran su.

A ɓangaren finafinan Hausa masu kyau da ma’ana da inganci da tafiya tare da zamani, Ali Nuhu ba shi da sa’a a Kannywood, don kuwa kamfanin sa ya doke na kowa wajen samar da labarai masu ƙayatarwa.

Tabbas, ‘yan fim na Arewa sun more kuma za su yi dariya gami da murnar samun tagomashin wannan muƙami da aka ba wa Sarki Ali Nuhu na MD na Nigerian Film Corporation (NFC).

Ali Nuhu mutum ne mai zumunci da karamci da mutunci da son haɗa kan ‘yan Kannywood. Abin da na faɗa zai tabbatar maka da hakan musamman a taron dina da aka haɗa masa. ‘Yan wasan Hausa tsofaffin jarumai da aka manta da fuskokin su mata da maza sun halarci wajen bikin don nuna murna da matsayin da ya samu a Gwamnatin Tarayya.

Ina mai kyautata zaton wannan matsayin da Ali Nuhu ya samu zai sake ɗinke duk wata ɓaraka da ta ke cikin Kannywood tare da samar da gagarumin cigaba ga masana’antar da ba a taɓa samun irin ta ba. In-sha Allahu!

Allah ya ba wa Sarki Ali Nuhu ikon aiwatar da hukumar da aka ba shi aiki cikin jin daɗi da kwanciyar hankali tare da kwatanta adalci ga kowa da yake ƙarƙashin ikon sa na masana’antar fim gaba ɗaya, Nollywood da Kannywood.

* Malam Abdullahi Jibril Ɗankantoma (Uncle Larabi) marubuci ne kuma ɗan kasuwa a Kano

 

Back to top button
error: Content is protected !!