Ali Nuhu Kawai Nake Da Burin Aura A KannyWood
Idan Akwai Namijin Da Zan Aura A Masana’antar KannyWood To Bazai Wuce Ali Nuhu Ba. – Jaruma Radeeya Jibril
Jarumar KannyWood Radeeya Jibril Ta Bayana Cewa Idan Akwai Wani Da Namiji Da Take Da Burin Aura A Masana’antar KannyWood To Bazai Wuce Ali Nuhu Ba.
Jarumar Ta Bayyana Hakan Ne Cikin Wani Shiri Da Ta Bakunta Na Gidan Radiyo Inda Mai Gabatarwa Ya Tambayeta Shin Duk Cikin Masana’antar KannyWood Idan A Bata Dama Wane Jarumi Ne Zata Iya Aurensa.
Sai Ta Bada Amsa Da Cewa Kaf Masana’antar KannyWood Ali Nuhu Ne Zata Iya Auranta Lokaci Guda Ba Tare Da Wani Bata Lokaci Ba.
Inda A Sake Tambayarta Ko Me Yasa Take Son SarKin KannyWood Din. Sai Tace Saboda Shi Tunda Yayi Aurensa Ba.a TabaJin Ya Sami Matsala Da Matarsa Ba. Ita Hakan Yana Daya Daga Cikin Dalilan Da Tasa Take Son Ali Nuhu.
An Sake Tambayarta Shin Zata Iya Komawa Gidan Mijinta Dasu Rabu Dashi, Kuma Ta Zauna, Inda Tace A.a Sam Bazata Iya Komawa Gidan Mijinta Ba Domin Kota Koma Bazata Iya Zama Ba.
Daga Karshe An Tambayaeta Alaqar Dake Tsakaninta Da Mai Gidanta A Harkar Fina Finai. Wato Shaba, Sai Ta Bayyana Cewa Akwai Aqala Mai Karfi A Tsakaninsu Dashi.







