Kannywood

Ali Jita Ya samu kambun awardin shekara Daga Tozali Magazine

Fitatcen mawakin Arewa Ali Jita ya samu kambun mawakin shekara daga gidan Jaridar Tozali wanda su ka gudanar a birnin tarayya Abuja tare da karrama wasu mawakan, dattawa, yan siyasa da yan Northflix na ruwaito.

Anyi bikin karramawar ne mai suna Henna Ball & Award Night a dakin taro na international conference center Abuja, ranar Asabar bakwai ga watan shabiyun shakerar nan.
Taron dai ya kunshi abubuwa da dama a ciki kamar al’adun kasar Hausa tare da wasu ababen nishadi da su ka hada fuskokin manyan kasar nan ciki akwai uwar gidan Gwamnan jihar kaduna Hajiya Ummi Nasir Ahmad El-Rufai da kuma uwar gidan gwamnan jihar kebbi Hajiya Dr Zainab Bagudu tare da Gen. kukasheka da kuma dan Majalisar Tarayya Hon Gudaji kazaure, Duk a wajen taron.

An karrama Ali Jita ne da kanbum mawaki mafi tashe na wannan shekara.

Ya karbi wannan karramawar ne sakamakon wasu jerin wakokin da ya saki a wannan shekarar wadanda su ka hada da Aboki, Arewa Angel, a sha ruwa, Maryam Gimbiya, Mama da dai sauran su.

An haifi mawakin ne a unguwar gyadi-gyadi da ke birnin Kano a watan Yuli na shekarar 1983.

Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a makarantar Army Day a tsakanin Jihar Lagos da kuma birnin taraiya Abuja. Ya ci gaba da karatun difuloma a fannin gudanar da aikin gwamnati da kuma kimiyar fasahar sadarwa duk a School for Management Studies da ke garin kano.

Mawakin na zaune ne a birnin Kano da mata daya da kuma da daya.

Ali Jiya ya fara sakin wakokinsa a albom ne a shekarar 2009 mai suna Jita. Tun wannan lokacin zuwa yanzu Mawakin ya kasance daya daga cikin jagororin mawakan Hausa a masana’antar finafinai da wakokin Hausa ta Kannywood.

Back to top button
error: Content is protected !!