Kannywood
Alamun Dasu Nuna Adam A Zango Zai Aure Fati Washa
A baya dai mun kawo muku Rahoton dake cewa Adam A. Zango ya bayyana zai kara aure kuma ‘yar Fim ce zai aura.
Adamun ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram saidai daga baya ya goge wannan sako.
A baya Adamu da Fati Washa sun sha soyayya wanda kiris ya rage a yi aure amma avin bai tabbata ba. Saidai a yanzu bayan yin waccan maganar tasa, Adamu ya saka hotonsa dana Fati Washa a Profile Picture dinsa na Instagram da alamar zanen Zuciya, dake alamta Soyayya.
Adamun dai bai yi karin haske game da hakan ba, amma lura da maganar da yayi kwanakin baya ana iya cewa watakila Fati Washa din ce zai aura.
Daga HutuDole