Kannywood

Al- Ameen Dagash Ya Fallasa Asirin Sadiya Haruna

Bayan na kalli Faifan Bidiyon da Sadiya Haruna, ta Saka a Shafin Sada Zumunta na Zamani tana Ambatar Sunana da cewa mun Cuceta gaskiya da Ban so ince komai ba, amma ganin yadda Masoyana suke ta Kira suna Tambaya sai naga ya kamata in yi Magana.

Abin da ya faru shi ne, Sadiya Haruna ta Kira ni a waya cewan Tana Son in yi Mata aikin Film din ta amma da ta fadamun ranar sai nace Ranar ce za a daura mun Aure Dan haka muka sake wata rana.

Muna cikin Tattaunawa na tambayeta Ina ne Wurin da za a yi aikin Tace mun Maiduguri, kuma lokacin Ana tsananin Yayin Boko Haram amma haka na kama hanya bayan mun Isa muka kirata aka dauko mu zuwa Masauki.

Na kalli Masaukin Na ce Gaskiya ba Zan iya zama a nan ba domin waje ne na Karuwan da suka mayar da kansu abin Sana’a, Inji shi.

Daga nan ni da Alasan Kwalle, muka Kira Mutanen mu suka canza mana Masauki, gari na wayewa ta zo ta same mu muka ce to a fita aiki domin muyi mu gama.

Nan fa ta kama kame-kame har dai muka fahimci Ashe ma Ko Inda za a yi Film din ba ta da shi kuma ba ta tanadi komai ba Yaudarar mu kawai tayi.

Tun da mun riga mun zo sai muka sake Kiran Jama’ar mu muka nemi alfarmar su suka nema mana wajen da muka shirya wannan film har muka gama mu ke ciyar da kanmu da duk wani daukar nauyi alhali kafin zuwan mu ba haka muka yi alkawari da ita ba.

A takaice dai akwai Sauran Kudi na da kudin Alasan Kwalle, da ba ta ba mu ba da muka tambayeta ta ce bari ta je ta kawo daga nan tayi Batan dabo har muka bar garin shine kuma sai muka ji wannan Tabarmar Kunyar tana nade ta da Hauka.

Amma Yanzu mun Mika Batun ga Jami’an Tsaro domin su damkota domin ta fuskanci Shari’a, na Ba ta Suna, da Kuma Biyan diyya, sannan kuma ta Ba mu cikon Kudin mu, Inji shi.

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng
Back to top button