Labarai

A’isha Yesufu Ta Buƙaci A Soke Majalisar Dattawa A Najeriya

Tsadar Gudanar Da Mulki: A’isha Yesufu Ta Buƙaci A Soke Majalisar Dattawa A Najeriya

Fitacciyar ‘yar fafutukar kare hakkin jama’a Aisha Yesufu, ta yi kira da a soke majalisar dattawan Najeriya domin rage tsadar harkokin mulki.

Aisha Yesufu, wanda ta kafa kungiyar Bring Back Our Girls Movement, tayi wannan kiran ne a wata hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya A Yau Lahadi a Legas.

Ta na mai mayar da martani ne kan kiraye-kirayen da ake yi a wasu sassan kasar na cewa, ya kamata kasar nan ta yi watsi da ‘yan majalisunta na biyu, ta kuma amince da ‘yan majalisar wakilai na bai daya domin rage tsadar harkokin mulki.

Mai fafutukar tace Najeriya za ta iya, Tunanin sake ɓullo da tsarin Gwamnati na majalisar dokoki domin rage makudan kudaden da ake kashewa a majalisar dokokin kasar.

“Muna buƙatar mu nazarci dimokuradiyyar mu da gaske, mu duba abin da ya dace da mu, mu yi wa talakawa hidima

Aisha Yesufu Ta ce an mayar da majalisar dattijai ta zama “gidan ritaya ga gwamnonin da ba su da kwarewa da Gazawa waɗanda ba su yi wa al’ummar jiharsu komai ba”.

A cewarta, kasar Senegal na gudanar da majalisar dokoki kaɗai, Bayan da ta soke Majalisar Dattawa a karo na biyu a watan Satumban 2012.

Tace: “Majalisar Wakilai tana da ikon kula da Harkokin samar da doka a ƙasa, sa ido da sauran abubuwan da ɓangaren Gwamnati ke yi.

Back to top button
error: Content is protected !!