Labarai

Ahmed Musa Ya Jajantawa Iyalan Waɗanda Su Ka Rasu A Ƙauyen Tudun – Biri A Harin Bom

Shahararren Ɗan Ƙwallon Ƙafar Nageriya Captain Ahmed Musa Ya Jajantawa Iyalan Waɗanda Su Ka Rasu A Ƙauyen Tudun – Biri A Harin Bom

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Kaftin Ahmed Musa MON ya na miƙa saƙon jaje da ta’aziyya ga iyalai, mai alfarma sarkin musulmai, gwamnatin Jihar Kaduna da al’ummar Nageriya gabaɗaya bisa iftila’in da ya afkawa al’ummar musulmai masu taron Maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

Kaftin Ahmed Musa ya bayyana lamarin a matsayin wani abin tashin hankali matuƙa wanda ya zama wajibi ga gwamnati ta gudanar da bincike na haƙiƙa tare da hukunta duk waɗanda aka samu da laifi bisa ganganci gami da ɗaukan matakan hana faruwar hakan a gaba.

A cewarsa, “Zuciyata ta girgiza matuƙa raina ya sosu da na samu labarin cewa sama da mutum 100 sun mutu a wannan iftila’i, ina addu’ar Allah Ya ji ƙan waɗanda su ka mutu Ya ba wa waɗanda su ka jikkata lafiya”. Cewar Captin Ahmed Musa.

Back to top button
error: Content is protected !!