Kannywood

Afakallahu Ya Aikewa Ado Gwanja Takardar Gayyata

Shugaban Hukamar Tace Fina Finai Ta Jihar Kano. Isma’il Na’abba Afakallah. Ya Aikewa Mawaki Ado Gwanja, Takardar Gayyata Kan Wakarsa Ta “CHASS”

Hakan Na Nufin Ana Bukatar Mawakin Yaje Ya Kare Kansa A Hukumar Tace Fina Finai Na Jihar Kano Kenan, Kan Sabuwar Wakar Tashi Da Ake Zargin Zata Bata Tarbiyya Musanman Ma Na ‘Ya ‘ya Mata.

Sai Dai A Wata Hira Da Akayi Da Mawakin Ya Bayyana Cewa Shifa Wakarsa Ba Ta 6ata Tarbiyya Bace, Kuma Baya Yita Da Niyyyar 6ata Tarbiyyar Kowa Ba, Yayi Wakarsa Ce Domin Nishadi Kuma Don Neman Abincinsa.

Yan Jarida Sun Sami Tajin Bakin Mawakin, Inda Ya Kare Kansa Kan Wanann Wakar Tun Kafin Ya Gurfana A Gaban Hukumar Na Tace Fina Finai, Wanda Isma’il Na’abba Afakallah. Ke Jagoranta.

Back to top button