Adam Zango Yana Shigowa Kano Zamu Kamashi – Kannywood
Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano Malam Isma’il Na Abba Afakallahu ya jaddada aniyar sa ta cewa muddin jarumin Finafinan Hausa Adam Zango ya shigo garin Kano sai Hukumar ta yi ram da shi.
Hakan ya biyo bayan wata sanarwar jarumin da aka gani a shafin jarum Rahama Sadau a Instagram, inda aka ga Zango yana sanar da masoyan sa cewa zai shigo garin domin kallon sabon shirin nan mai suna ”Mati A Zazzau” wanda ake nunawa a Film House Cinema Kano.
A bidiyon jarumin ya kira ga masoyan sa, da su hadu da shi a ranar Lahadi da kuma ranar Litinin domin kallon shirin tare da shi.
Wani bayanan sirri da kafar watsa labarai ta ‘Kannywood Exclusive’ ta samu shi ne, Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta gama shirin ta na musamman domin kama jarumin muddin ya shigo silimar wurin kallon shirin, kasancewar jarumin ya ki yin rijista tare da bin sauran ka’idojin hukumar.
Da ya ke yi mana karin bayanin game da zargin da ake yi wa hukumar na shirin kama Zango, shugaban Hukumar Malam Isma’il Na Abba Afakallahu ya ce, Kano ta na bambancin da sauran jihohin Arewa. Sannan hukumar tace Finafinai an kafata ne domin tsaftace addini da kuma al’adar jihar Kano.
Don haka duk mutumin da ya yarda zai girmama al’ummar Kano dole ne ya bi dokokin su wanda majalissa ta tabbatar da su tun a shekarar 2001.
Afakallahu ya ci gaba da cewa, duk mutumin da bai yarda harkar fim hanya ce ta sadarwa da za ta haskaka addini da al’ada ba ta yadda mutanen Kano suke, ko wanene shi mun hakura da shi ko da kuwa kyamara ce ta haife shi.
Shi wannna jarumin ya yi bayanin cewa ba zai yarda ya bi wannan ka’idoji ba, kuma ba zai girmama su ba, to mene ne zai nunawa mutanen Kano da har zai cewa masoyan sa su yi gangami, me ya ke da shi da zai gabatar akan su?
Dokar mu ita ce, duk mutumin da bai yi rijista ba, babu wani abu da zai taso na jihar Kano ya zo yace zai yi mu kuma mu zuba masa ido mu kyale shi bai isa ba, ko ma wanene.
Shi daman ya ce babu ruwan sa da Kano, to ka ga kenan bai da hurumin da zai shigo ya yi wani abu da hukuma ta ke da hurumi da shi.