Adam A Zango Ya Fitar Da Sabuwar Hanyar Kallon Fina Finan Sa
Jarumi kuma mawaki Adam A Zangoya bayar da sanarwa ga masoyansa na cewa daga yanzu zai dinga sakin fina-finansa a yanar gizo wato shafin YouTube.
– Jarumi kuma mawaki Adam A Zangoya bayar da sanarwa ga masoyansa na cewa daga yanzu zai dinga sakin fina-finansa a yanar gizo wato shafin YouTube
Jarumin ya bayyana hakan ne bayan sanarwar da ya bayar a makonnin baya na cewa ya bar kungiyar fina-finan Hausa ta Kannywood
Ya ce daga yanzu duk mai sun kallon fim dinsa zai shiga shafinsa na YouTube ne ya kalla fim din a ciki
Tsohon fitaccen dan wasan Kannywood kuma mawaki Adam A Zango ya bayyana cewa daga yanzu zai dinga sakin fina-finan sa ne a yanar gizo ma’ana YouTube domin masu kallo su je su kalla a ciki.
“Daga yanzu duka fina-finan da zanyi zan dinga saka su a shafina na YouTube.”
Jarumin ya ce zai fara sanya fim dinsa na farko wanda zai yi mai suna ‘Gudun Mutuwa’ wanda zai saki a ranar 10 ga watan Oktoba.
Sannan jarumin ya bayyana hanyar da dukkanin masoyansa da masu bukatar kallon fina-finansa za su dinga kallon fim dinsa a shafin YouTube.
Da farko dai duk mai son kallon sabon fim din ‘Gudun Mutuwa’ zai aika da naira dubu daya (N1000) ga asusun banki wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram, ko kuma ka aika da katin waya na naira dubu daya zuwa layukan da ya wallafa a shafin nasa.
Idan mutum yayi haka ranar da za a saki fim din za a tura masa da link da zai yi amfani da shi wajen kallon fim din.
“Ina kira ga dukkanin masoyana da su aiko da kudinsu domin samun daman kallon fim din. Bayan haka kuma daga yanzu zan dinga sanya fim dina ne a yanar gizo wato YouTube.”