Bidiyon ya bazu a soshiyal midiya kamar wutar bazara, kuma ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sharhi.
Zango ya yi ƙaurin suna wajen auri-saki, domin kuwa Safiyya ita ce mace ta shida da ya aura ya saki.
Da farko ya auri Amina ‘yar garin Kaduna a cikin 2006, ta haifa masa ɗan sa na farko, Haidar, wanda a bana ya cika shekara 16 da haihuwa.
Da ya sake ta, sai ya auri A’isha, wadda ‘yar’uwar sa ce ta jini, daga garin Shika da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Ta haifa masa ‘ya’ya maza uku.
Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga Jihar Nasarawa. Ita ma ya sake ta.
Sai ya auro jarumar Kannywood mai suna Maryam A.B. Yola daga unguwar Lugbe a Abuja a cikin 2013. Kafin nan sun fito tare a cikin fim ɗin ‘Nas’.
A cikin 2015, Zango ya tsallaka ƙasa zuwa garin Ngaoundere a Jamhuriyar Kamaru ya auro Ummul Kulsum. Ita ce ta fara haifa masa ‘ya mace, wadda ya raɗa wa suna Murjanatu.
Da ya sake ta ne ya auro Safiyya, wadda aka ɗaura auren sa da ita a ranar Juma’a, 26 ga Afrilu, a 2019 a masallacin fadar Sarkin Gwandu da ke garin Gwandu a Jihar Kebbi.
Sun haifi ‘ya mai suna Furaira (sunan mahaifiyar sa), wadda ake wa laƙabi da Diana, a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.
Diana ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan Adamu (maza huɗu da mata uku), kuma abin lura shi ne kowane ɗa uwar sa daban.
A lokacin da aka yi auren Zango da Safiyya, mutane sun taya su murna, yayin da wasu ke tababar ɗorewar auren saboda yadda ake kallon jarumin a matsayin mai auri-saki.
Mujallar Fim ba ta san takamaiman dalilan mutuwar aurarrakin Zango guda biyar ba, amma ya faɗi dalilin saɓanin sa da Safiyya.
A cewar sa, ta na kasuwanci irin na intanet ne a asirce ba tare da sanin sa ba, kuma da ya hana ta sai ta ƙi bari, tare da ɗaurin gindin ‘yan’uwan ta.
A bidiyon da ya wallafa a cikin Fabrairu, ya ce: “Tunda sun zaɓi kasuwancin da ta ke yi fiye da zaman auren ta, ba ni da zaɓi. A kowanne lokaci daga yanzu, za a ji labari mara daɗi. A gafarce ni, wannan shi ne.
“Saboda ina sananne ba zan kashe kai na saboda mabiya na ko masoya na in birge su ba in ci gaba da zama da baƙin ciki saboda babu yadda na iya.”
Sai dai kuma binciken da mujallar Fim ta yi ya gano cewa babban abin da ya farraƙa ma’auratan shi ne soyayyar da Adamun ya yi da jarumar shirin sa mai dogon zango da ya ke shiryawa mai suna ‘Asin Da Asin’, wato Meera Shu’aibu, wadda aka fi sani da Junaidiyya ta cikin diramar ‘Gidan Badamasi’.
Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunan ta ta faɗa wa mujallar Fim cewa Meera ta zama silar mutuwar wannan auren ne saboda soyayyar da Zango ya yi da ita ce ta jawo saɓani tsakanin sa da Safiyya wanda har ya kai matar tasa ga barin gidan auren ta a Kaduna, ta koma Kebbi.
“Meera ta so auren Adamu, kuma shi ma haka, amma sai ya kasance mahaifiyar sa ba ta so, sannan shi ma ya yi wani bincike, saboda haka dai ya haƙura da auren ta,” inji majiyar.
Majiyar ta ce Safiyya ta bayyana cewa “ita ba ta damu da soyayyar sa da Meera ba in da auren ta zai yi, amma ba yadda su ke yi ba.
Majiyar ta ƙara da cewa, “A lokacin da Soffy ta koma Birnin Kebbi, Meera ta riƙa faɗa ma mutane cewa saboda ita ne Soffy da Adamu su ka samu saɓani.
“To amma ba su tare yanzu, soyayyar tasu ta tarwatse. Kuma Meera ta lashi takobin cewa Adamu da Soffy ba za su taɓa sasantawa ba tunda har ya ci amanar ta.”
A bidiyon da ya saki a farkon wannan shekarar, Zango ya nuna ya san irin kallon da mutane su ke masa na aure-aure, har ya sha alwashin in dai har auren sa da Safiyya ya mutu to bai ƙara yin aure ba har abada.
Ya ce: “Ina ganin na gama aure. Da izinin Allah na gama aure, kuma ina roƙon Allah ya kare ni daga dukkanin abubuwan da na ke gujewa ya sa na ke ta yin wannan auren.”
To, yanzu da auren ya mutu za a zuba ido a ga idan zai ƙara yin auren ko a’a, da kuma irin rayuwar da zai yi ba tare da aure ba a matsayin sa na matashi mai jini a jika.
Musa Nuhu