E News

Abubuwan Daya Kamata Ku Sani Game Da Facebook Monetization

Abubuwan Daya Kamata Ku Sani Game Da Facebook Monetization.

Ko a lokacin da Shugaban Sashen Hulda da Kasashe na kamfanin Meta, Sir Nick Clegg ya zo Najeriya da kasar Kenya in da ya yi busharar fara biyan masu shafuka a sahar Facebook da Instagram idan su ka cika ka’idojin da ake bukata, ya ambaci watan June (Yuni) ne kawai, amma bai fadi takamaimai rana ko lokacin ba. Wadda wannan ya sanya, da dama daga cikin masu jiran fara cin gajiya (content creators) su ka kagu tare da zumudi tun da aka shigo watan na June. Wadda tsallakowa kwanaki 20 na watan ya sanya da dama fara karaya ko ma cire tsammani kan tabbatuwar lamarin.

Sai dai abun da ya kamata mu fahimta anan shine, zai yi wahala kamfani kamar na Meta ya fitar da sanarwa a Hukumance, sannan ya zo ya saba ba tare da kuma gabatar da wani uzuri ko dalili ba.

Wannan ta sa bayan dadewa da cike ka’idoji a biyu daga shafuka na (Facebook pages) ban taba cire tsammani ba.

Kuma daga karshe dai sun cika alkawarin da su ka yi wa Najeriya da Kenyan.

Sai dai ya kamata mu kula sosai, fara biyan masu shafuka (Facebook Page Monetization) fa ba da sauki zai zo ba. Dole sai ka dage da samar da bidiyoyin ka na kan ka, ba na zari-ruga da za ka gani a waje ka kwaso ka zo ka kama wallafawa ba. Ko da kuwa bidiyo za ka dauka daga wani waje, to, ka tabbatar da ka yi wa Video din aiki ta hanyar kara wani abu da zai bambanta ta shi da asalin yadda ya ke ta hanyar nuna kwarewa a cikin sa (adding value) kamin ya zamo wadda za ka iya samun kudi da shi. Domin Facebook su ma kamar YouTube ne, ba sa lamuntar amfani da abu guda daya a mabambantan shafukan da yawa (reused content) a kan dandalin kuma duk su biya kowa daga wannan bidiyon.

Idan ka na son samu Kudi a Facebook dole sai ka cire lalaci ka samu wani abu muhimmi da mutane (audience/followers) za su so ka dinga yin sa ka na wallafawa a shafin ka (page). Kamin su dinga saka maka talla (In-stream Ads) a kai.

Duk da da yawa za su samun tarnakin cin gajiyar wannan dama da Facebook ta bayar sakamakon wani kuskure da wasu da yawa daga cikin mamallaka shafuka su ka yi, na cike bayanan su ba tare da kasar Najeriya na cikin halastattun kasashe ba a baya.

Wadda hakan a yanzu ya zamewa wasu matsalar da za ta hana su rawar gaban hantsi a fagen amfanuwa da lamarin har sai sun shawo kan matsalar ta PRE-ENROLLED.

Zan zo da cikakken bayani game da abubuwan da su ka jawowa da yawan masu shafukan Facebook tarnakin amfana daga abun da za su samar a shafukan na su dalilin pre-enrolled.

Daga Shafin – Ahmad Nagudu

Active Media Labs

Back to top button
error: Content is protected !!