E News

Abubuwa Guda 7 Da Mai Shari’ar Da Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sunusi

Abubuwa Guda 7 Da Mai Shari’ar Da Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sunusi Yai Da Ya Zama Abun Zargi

1. Umarnin dakatar da nadin Sanusi II

A ranar 24 ga watan Mayu, Mai shari’a Liman ya bayar da umarnin hana Gwamna Abba Yusuf aiwatar da dokar da ta soke masarautun Kano ta shekarar 2019 wadda za ta mayar da Sarki Sanusi II kan kujerarsa.

2. Ana zargin Alkalin da rashin da’a

A ranar 16 ga watan Mayu ne hukumar shari’a ta kasa (NJC) ta sanar da karin girma ga alkalai 22 zuwa kotun daukaka kara ciki har da Mai shari’a A. M Liman.

Majalisar ta kara masa girma ne bayan ta yi watsi da karar da aka shigar kan Mai shari’a Liman da wasu alkalai 34 bisa zargin rashin da’a a aiki, in ji rahoton Vanguard. 3.

Kawo tsaiko a dakatar da Ganduje Mai shari’a Liman ya bayar da umarni a ranar 18 ga Afrilu na hana a dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

4. Alkalin da ya hana kama Ganduje

Mai shari’a Liman a ranar 8 ga Yuli, 2023, ya hana hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano tuhuma, kamawa, gayyata ko tsare Ganduje. Umurnin ya biyo bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na yin bincike kan wani bidiyo na 2018 da ake zargin Ganduje yana karbar makudan kudi daga hannun wani dan kwangila. 5. ‘Dan takara ya zargi Alkali Liman A shekarar 2022, dan takarar jam’iyyar NCP a zaben gwamnan jihar Edo na 2020, Peters Osawaru Omoragbon, ya zargi Mai shari’a Liman a bainar jama’a da “rashin da’a.

6. DSS ta kama alkalai a 2016 Mai shari’a

Liman na cikin alkalan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kai samame gidajensu bisa zargin karbar cin hanci da rashawa a shekarar 2016.

Jaridar The Cable ta ruwaito gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya hana a kama Liman, amma dai hukumar DSS ta yi zargin cewa ta kwato dala miliyan 2 a gidansa na Fatakwal.

Da yake mayar da martani, alkalin ya ce bai taba ganin irin wannan adadin kudin ba, yana mai yin nuni da zai yi murabus daga aikin idan har ya mallaki wadannan kudi, in ji Daily Post.

7. Shari’ar rashawar N25bn ta Igbinedion A Afrilun 2015, Mai shari’a Liman da ke jagorantar wata babbar kotu a Edo, ya karbi shari’ar cin hanci da ta hada da Michael Igbinedion, kanin tsohon gwamnan Edo, Lucky Igbinedion.

~ LEGIT

Back to top button
error: Content is protected !!