Abinda Yasa Ba’a Ganina A Harkar Fim – Aminu saira
Duk A Cikin Shirin ‘Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
An samu lokaci mai tsawo ba a ganin fitaccen Darakta Aminu Saira a cikin harkar fim, wannan ta sa ake tambayar ko dai ya hakura da harkar ne gaba daya.
Kasancewar sa jigo a cikin harkar ne ya sa daina ganin na sa a cikin harkar ya zama abin tambaya a wajen muta ne.
Wakilinmu Mukhtar Yakub Ya ji ta bakin Darakta Malam Aminu Saira dangane da rashin ganin na sa, in da ya ba mu amsa da cewar.
“Ba wai rabuwa aka yi da gani na ba, sai dai a ce ba a gani na kamar yadda ake gani na a baya, kuma ita rayuwa, komai canzawa ya ke yi, don haka kada ka zagi zamani, domin ko yaushe idan duniya ta canza, ya kamata ku ma ku canza.
Domin haka yanzu idan ka duba yadda tsarin masana’antar mu ya ke na a bugo plate CD a kawo kasuwa, to gaskiya, kusan duk duniya an daina, an rabu da wannan tsarin, kuma shi kasuwancin nan da a ke yi, ana yi ne don a karu.
To matukar za a yi ta sakin kudi a kasuwa ba ya dawowa, to wata rana durkushewa za a yi gaba daya, kuma idan aka tafi a haka, Su masu tasowa, wanne gata aka yi musu, yadda za su samu masana’antar a yanayi mai kyau?
To gaskiya wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka karkata don mu ga wanne hanyoyi ne za a samar domin a dora masana’antar a kan turba, don haka ne ba a gani na, amma dai har yanzu mu na cikin harkar fim ana damawa da mu mun koma wani bangaren ne domin samar wa harkar mafita.
Kuma da zarar komai ya daidaita za mu dawo mu ci gaba da sabon tsarin da za mu dora masana’antar don ta ci gaba, amma dai ba zai yiwu ba a zauna cikin halin da harkar ta ke ciki a yanzu, dole a samar mata da mafita”.
Daga karshe ya yi kira ga abokan sana’ar sa da su hada hannu waje guda domin kawo sauyin da masana’antar ta ke bukata.
Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya