Kannywood

Abinda Maza Ke So A Jikin Mace Mai Kyau Irina Shine Su Auremu Su Gama Jin Dadinmu

A wata hira da aka yi da tsohuwar jaruma Fati KK ta bayyana cewa abinda maza ke bukata a jikin mace mai kyau irinta shine su aureta su gama jin dadinta su sake ta

Ta ce yanzu ita tsoron sake yin aure take yi, saboda tana kallon maza duka halinsu daya ne

– Ta bayyana cewa ta fito daga wajen iyaye da suke da fahimta ga kuma ni’ima ta addinin Muslunci ita ce ta saka kullum take yiwa Allah godiya

Fati KK tsohuwar ‘yar wasan fina-finan Hausa ce ta Kannywood wacce bata bukatar muyi dogon labari game da ko wacece saboda sunan da tayi lokacin da take masana’antar. ‘Yar asalin garin Kontagora ce dake jihar Neja. A lokacin da tauraruwar Fati ke haskawa kawai sai aka nemeta aka rasa abinda yasa masoyanta wasi-wasin inda ta shiga.

A wannan hirar da ta yi da Aliyu Askira wakilin jaridar Blueprint, ta yi bayani akan auren, da kuma dawowar ta harkar fina-finan Hausa.

Blueprint: Menene sirrin wannan kyau din da kika kara?

Fati KK: Farko dai zan iya cewa ina farin ciki na samu iyaye wadanda suke da fahimtar rayuwa, da kuma addinin Musulunci, addinin da yake nuna mana cewa duk abinda ya faru da kai ka dauke shi a matsayin kaddara. Na biyu na dawo harkar fim kuma abokanan aikina sun karbe ni hannu biyu-biyu, saboda haka dole zaku ganni cikin farin ciki. Haka kuma bayan aure sau biyu bazan iya cewa zan koma na cigaba da zama da iyayena ba, saboda ina kannai da suma suka taso suke bukatar kulawa.

Blueprint: Kinyi aure sau biyu, sannan kina da ‘yaya uku. An yi zargin cewa mijinki na biyu ya yaudareki ne ta inda ya nuna cewa yana da kudi kuma abin ba haka yake ba. Me zaki ce akan wannan maganar?

Fati KK: Kamar yadda ka bayyana, gaskiya ne na samu matsala da dukan su, amma hakan ba zai sa na ci musu mutunci ba ko na kira sunayensu. Kaddara ta saka nayi aure sau biyu kuma duka na samu matsala. Nayi iya bakin kokarina a matsayina na mace domin ganin daya daga ciki ya dore, amma abin ya ci tura, kalleni da kyau ka gani menene namiji yake nema a jikin mace da babu a jikin Fati KK? Na yi iya yina abin yaci tura, kuma babu yadda za’ayi mace da tayi aure sau biyu ta fito ta dauki kafa ta koma gaban iyayenta domin su cigaba da kula da ita. Zan ce gaskiya kuma ina jin tsoron sake yin aure a karo na uku, saboda ina ganin cewa maza duka halinsu daya, abinda suke so a jikin mace mai kyau irina shine su auremu idan suka gama jin dadinmu sai su sake mu su nemi wata.

Back to top button
error: Content is protected !!