Labarai

Abin Daya Kamata Ku Sani Game Da TAHAJJUD

Abin Daya Kamata Musulmi Ya Sani Game Da Sallar Tahajjud

A Cewar Malam Sukairaj Hafiz Imam:

“Idan Ni zan yi Limancin sallar Tahajjud sharaɗin farko da nake sakawa dole a kashe “Speakers” na waje a bar iyaka na cikin Masallaci kaɗai.

Shari’ah ta bawa kowa haƙƙinsa, wanda yake so ya yi barci bai kamata a takura masa ba, in ba haka ba za a yi tufka da warwara.

Ita sallar dare akwai yadda Ma’aiki Sallallahu alaihi wa sallama ya koyar da yadda ake yinta.

Wasu suna zuwa Masallaci da daddare, rabi Sallah rabi ‘chat’ ko hira ko barci. Ka yi barcinka a gida shi yafi maka alheri.

Wani zai fita sallar dare amma ya kasa zuwa Asuba Ka yi barcinka a gida shi yafi maka alheri.

Wani zai zo Masallaci yana ƙorafin Liman ya yi dogon karatu, har ransa ya baci. Ka yi barcinka a gida shi yafi maka alheri.

Ki yi Sallah a ƙarshen ɗakinki, gaban gadonki shi yafi miki alheri akan zuwa Masallaci.

Ki fita Sallah amma ki tafi wajen saurayi zance; toh zunubinki hawa uku ne. Sabon Allah, Sabon Iyaye d kuma keta alfarmar watan Ramadan. Ki yi barcinki a gida shi yafi alheri.

Kafin ka aikata kowana aiki ka nemi ilimin yadda ake yinsa don gudun kar ka yi tufka da warwara.

Bautar Allah ana yinta ne kaɗai akan ilimi ba wai yadda mutum yake so ba.”

Daga Sukairaj Hafiz Imam

Back to top button
error: Content is protected !!