Abin Daya Kamata Ku Sani Game Da Kudirin Takaita Kiwo a Nigeria
Abun Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Kudirin takaita kiwo a Nijeriya, kudirin da idan ya zama doka zai kori Fulani Makiya jihohinsu na asali.
Kudirin dokar kafa hukumar kiwo ta kasa ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattawa a ranar laraba 5 ga watan 6 bayan wata muhawara mai zafi.
Kudurin dokar dai na da nufin kafa wuraren kiwo na makiyaya a jihohinsu na asali, wanda zai maye gurbin kiwon da suka yi a fili a ko ina a halin yanzu.
Idan har aka kafa dokar, hukumar za ta sa ido kan yadda ake gudanar da kiwo da kuma kula da kiwo a fadin kasar nan.
A muhawarar da ya gabatar, wanda ya dauki nauyin kudirin dokar, Sanata Titus Tartenger Zam ( Dan APC, daga jihar Benue), ya ce samar da wuraren kiwo a jihohin da makiyaya suka fito zai hana tashe-tashen hankula da kuma samar da zaman lafiya.
Kafin dokar ta karade karatu na biyu, ta fuskanci kakkausar adawa daga wasu Sanatocin Arewa, inda suka dage cewa a bai wa makiyayan ‘yancin zama a ko’ina a Najeriya, kamar yadda sashe na 41 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tabbatar.
Sanata Adamu Aliero (dan PDP, daga jihar Kebbi) ya ci gaba da cewa killace makiyaya a jihohinsu ya saba wa tsarin mulkin kasar.
Aliero ya kuma ce ya kamata a kafa wuraren kiwo a matsayin sana’o’i masu zaman kansu wadanda ba sa bukatar shigar da gwamnatin tarayya ta hanyar kafa hukumar.
Ya ce dalilin da ya sa zai goyi bayan kudurin dokar shi ne a kawar da tanadin da ya takaita kiwo zuwa jihohin makiyayan na asali.
Sanata Mohammed Goje (dan APC, daga Gombe) ya bayyana kudurin a matsayin wariya, inda ya ce kiwon shanu ya fi kyamari a Arewa.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata a samar da dokar da zata ta amfani kasar baki daya, ba wai kawai wani yanki na musamman ba.
Shi ma Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu (dan NNPP, daga Kano) ya bayyana damuwarsa kan kudirin da ke tauye hakkin makiyaya.
Sanata Hussein Babangida Uba (Jigawa Arewa-maso-Yamma), ya yi kira da a yi taka-tsan-tsan wajen zartar da kudirin, duba da yadda aka rika samun sabani a baya.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya sake nanata cewa duk ‘yan Najeriya na da ‘yancin zama a ko’ina a kasar.
Ya ce maganar makiyaya su koma jihohinsu na asali ya saba wa tsarin mulkin kasar. Ya ba da shawarar a sake duba kudirin don ya dace da tsarin mulki.
Barau ya ce, “Akwai tuggu a cikin wannan kudiri, akwai matsala domin ba za ka iya hana kowane dan Najeriya zama a duk yankin da yake so ba. Yanzu in gaya musu su koma jiharsu ta asali, ina ne asalin asalinsu?
Sai dai Sanata Enyinnaya Abaribe (dan APGA,daga Abia) ya goyi bayan kudurin a matsayin mafita ga rikicin manoma da makiyaya, amma ya ba da shawarar a yi wa kundin tsarin mulki da dokar amfani da filaye gyaran fuska don kyautata tsarin tafiyar da filaye.
Abaribe ya lura cewa yayin da wasu makiyayan ke zaman lafiya kuma suna sana’ar halastacciyar sana’ar dabbobi, akwai kuma wasu miyagu da ake daukar nauyinsu domin tada zaune tsaye.
Sanata Sunday Karimi (dan APC, daga Kogi) ya ba da shawarar cewa kowace jiha ta kafa wuraren kiwon dabbobi domin magance matsalar kasa yadda ya kamata.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira da a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a domin hada da bayanai daga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu kiwon shanu da gwamnatocin jihohi.
Ya ba da tabbacin cewa za a yi kokarin cimma matsaya kan kudirin, gami da gyare-gyaren da suka dace kan dokar amfani da filaye.
An mika kudirin dokar ga kwamitin hadin gwiwa kan harkokin noma, shari’a, da kuma harkokin shari’a na majalisar dattawa domin yin nazari a kai, tare da gabatar da rahoton cikin makonni hudu.
An mika kudirin dokar ga kwamitin hadin gwiwa kan harkokin noma, shari’a, da kuma harkokin shari’a na majalisar dattawa domin yin nazari a kai, tare da gabatar da rahoton cikin makonni hudu.