Labarai

Abin Da Yakamata Ku Sani Game Da Fara Shigo Da Shinkafa

Abin Da Yakamata Ku Sani Game Da Batun Fara Shigo Da Shinkafa Najeriya Sabanin Yadda Wasu Suke Tunani.

Shinkafa

Daga Muhammad Kabir Aminu

Wato yadda na ga mutane suna ta murna za a shigo da Shinkafa har ta gaban gidan Manjo kamar fa ba haka lamarin yake ba.

Har yanzu dai gwamnatin ba ta ce ta buɗe kan iyakar Najeriya da wasu ƙasashe ta bada damar a shigo da kaya ta kan iyakar ƙasa ba, kawai cewa aka yi an bada dama ƴan kasuwa su yi canjin Dala daga CBN.

Wannan yake nuna da sauran aiki, domin ko a baya kusan ana shigowa da waɗannan kayayyakin amma ta ruwa ba ta kan iyakar ƙasa ba kawai banbancin shi ne an hana masu shigo da kayan canjin Dala ne aka kuma tsauwala haraji ta yadda kayan suka yi muguwar tsada, a nazarin tsohuwar gwamnati haka zai haɓɓaka masana’antun cikin gida.

Ina ganin mu jira mu ji me Hukumar dake yaƙi da fasa ƙwabri ta ƙasa (Customs) za ta ce akan lamarin.

Fatan Allah ya sauƙaƙa mana ya zaunar damu lafiya, Amin.

 

Back to top button
error: Content is protected !!