Kannywood

Abin da ya sa na daina sumbatar mata a fina-finan Nollywood – Ali Nuhu

Tauraron fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya ce ya daina sumbata ko rungumar mata a fina-finan kudancin Najeriya ne saboda hakan bai dace da al’ada da addininsa b

A hirarsa da BBC a shafin Instagram ranar Talata, shahararren dan wasan na fina-finai ya ce ba zai daina sana’ar fim ba.

Da yake amsa tamabayar da wani mai sauraronmu ya yi masa kan yadda yake fuskantar yanayin da zai iya kai shi ga runguma ko sumbatar mace a fina-finan Nollywood, Ali Nuhu ya ce “a shekarun baya idan ka lura na yi irin wadannan fina-finai amma daga baya da na ga korafe-korafen mutane, ka ga mutum jakada ne na Arewa…kuma Musulmi…shi ya sa ni yanzu ba na fitowa a irin wadannan fim din.”

Tauraron ya ce babu wanda ya taimaka masa da ko sisi lokacin da ya soma shirya fina-finai.

Ali Nuhu ya ce babu wanda ya taimake shi da ko sisi lokacin da zai soma shirya fim

A cewarsa, ba zai iya kayyade adadin fina-finan da ya fito a cikinsu ba saboda yawansu, yana mai cewa wasu daga cikin su ma ana sauya musu suna kafin su fito don haka ba zai iya rike sunayensu ba.

Wannan layi ne

Rayuwar Ali Nuhu a takaice

  • An haife shi a watan Maris na 1974
  • Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
  • Ya yi digiri a jami’ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999
  • Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
  • Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a fina-fina Nollywood
  • Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
  • Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki

Tauraron, wanda ake yi wa lakabi da Sarki a fagen fina-finan Kannywood, ya ce harkar fim ce abin da ya fi sani a rayuwarsa tun yana matashi har yanzu don haka babban burinsa shi ne ya ga an ci gaba da samun sauyi mai kyau a masana’antun fina-finai.

Ali Nuhu dai ya kwashe fiye da shekara 20 yana raka rawa a fina-finan Kannywood da Nollywood, inda ya lashe lambobin yabo a ciki da wajen Najeriya.

Back to top button
error: Content is protected !!