Iyalai

Abin Da Ya Sa Mata Suke Tsufa Da Wuri Bayan Sun Yi Aure

Na dade ina yin wannan nazarin game da rayuwar matan kasar Hausa, a kan dalilin da ya sa suke saurin tsufa da zaran an yi musu aure sun je gidan miji. Za ka ga yarinya karama wacce aka haife ta a gabanka da zaran ta isa aure an kai ta dakin miji, shekara daya kawai zuwa biyu bayan ta haihu idan ka gan ta abin zai ba ka tsoro da mamaki domin za ka gan ta duk ta tsufa ta yankwane kamar wata tsofuwa.

Abin da yake ba ni mamaki shi ne, kafin ‘yan matan su yi aure sun iya kama jikinsu da daukar wanka da kwalliya. Watakila wannan shi ne dalilin da ya sa samari suka yi wa matan ca a lokacin da suke gidan iyayensu. Amma da zaran ta shiga dakin miji, shi kenan wannan kama jikin da wannan wankan da kwalliya duka sun zama tarihi.

Musamman idan ta samu juna biyu ko kuma ta haihu a wannan lokacin wata matar ko abincin da ta dafa wani namijin mai tsantsami ba zai iya ci ba balle har ya yi hira ko hada shimfida da ita ba. Kuma a irin wannan yanayin ba kowane namiji ba ne zai iya zama da irin wadannan matan ba, dole sai dai cikin biyu a yi daya ko dai ya sake ta ko kuma ya karo aure.

Da yawa matanmu haka suke ba su damu da ado da gyaran jikinsu ba kamar yadda suke a lokacin suna ‘yan mata. Dalilin kenan da ya sa mazajensu ke gudunsu suna bin ‘yan matan waje ko karuwai. Domin matansu ba su yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen ‘yan matan waje ba. Kullum za ka tarar da mace da daurin kirji kai a cukurkude ya tsufa ba kitso ba tsafta.

Yadda take a hargitse haka ‘ya’yanta da dakinta da gidanta suke babu kulawa. Idan mijin ya yi magana domin ta gyara sai tace, “kawai ka gaji da ni ne duk shi ya sa kake ta yi min irin wannan tsangwamar. To ya kake son na yi ni inji ce da zan yi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa na yi wanka kuma na share dakin nan sannan na yi wa yaran nan wanka”.

Domin matansu ba su yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen ‘yan matan waje ba. Kullum za ka tarar da mace da daurin kirji kai a cukurkude ya tsufa ba kitso ba tsafta. Yadda take a hargitse haka ‘ya’yanta da dakinta da gidanta suke babu kulawa. Idan mijin ya yi magana domin ta gyara sai tace, “kawai ka gaji da ni ne duk shi ya sa kake ta yi min irin wannan tsangwamar. To ya kake son na yi ni inji ce da zan yi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa na yi wanka kuma na share dakin nan sannan na yi wa yaran nan wanka”. Babu yadda mijin ya iya dole sai dai ya yi hakuri ya daina gayyato abokansa gidan dan ka da su fahimci matsalar matarsa ko kuma ya fara tunanin sakinta ko kara aure. Abin da zai ba ka mamaki shi ne, irin wadannan kazamen matan idan suka tashi fita unguwa, idan ka gan su ba za ka iya gane su ba. Wanka suke dauka a yi kitso da kunshi da gyaran jiki kamar za ta gasar kyawawa.

Har kananen ‘ya’yansu sun gane su da zaren sun yi kwalliya to unguwa za a tafi sai ka ga yaran sun fara binsu suna yi musu kuka dan ka da iyayen su tafi su bar su a gida. Idan kuma aka yi rashin sa’a mazajen suka gaji suka sake su, idan suka fara zawarci sai kuma ka ga sun fara wanka da kwalliya. Wasu mazajen kuma za su dauke su a rashin sani, sai an yi auren kuma hali ya bayyana a sake sakinsu. To haka za a yi ta yi har ma karshe su rasa wanda zai aure su.

Wallahi mata wannan shi ne babbar matsalarku, shi ya sa kuke tsufa tun da kananen shekarunku.

Kuma shi ya sa mazajenku ke gudun ku ko auren ku ya mutu. Ku lura da kyau ku ga yadda Turawa da Larabawa da Indiyawa da kabilunmu wadanda muke zaune kasa daya haka suke yi? To dan Allah mata a daure a dinga wanka da kwalliya da tsafta, domin ba kowane namiji ba ne zai iya zama da kazamar mace irin wannan ba.

Kamar yadda kuke gyara jikinku kafin aure dan samari su gani su yaba, ya kamata ku gyara jikinku a gidajen mazajenku domin aurenku ya daure kuma ku zauna lafiya. Jikin mata ba irin na maza ba ne dole sai da gyarawa.

Daga LeaderShip Hausa

HausaStrea TV Apk

Back to top button
error: Content is protected !!