Abin Da Malam Ibrahim Daurawa Ya Fada Kan Murja Ibrahim Kunya,
Abin Da Malam Ibrahim Daurawa Ya Fada Kan Murja Ibrahim Kunya, Kan Raye Rayen Banza Da Kuma Karantun AlQur’ani Ba Dai Dai Ba.
Sabon Shugaban Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Sheikh Malam Ibrahim Daurawa Ya Bayyana Cewa Sunanan Sun Kafa Media Operations, Wato Fannin Dake Kula Da Mutanen Dake Harkokinsu Akan Shafukan Sada Zumunta.
Inda Su Wannan Fannin Suna Kula Ne Kan Mutane Musanman Mata Dake Fitsara Ko Kuma Tsalle Tsallen Banza A Shafukan Sada Zumunta.
Cikin Masu Kula Ne Sai Daya Daga Ciki Ya Kai Karar Ita Murja Ibrahim Din Inda Ya Bayyana Ma Shugaban Hukumar Na Hisbah. Kan Cewa Yaga Murja Tana Yawan Yin Raye Rayen Banza, Yakamata A Kamota Domin A Ganar Da Ita Kan Abin Da Takeyi Babu Kyau.
Daga Baya Sai Ya Sake Dawowa Domin Sanar Da Sheikh Daurawan Cewa Ya Sake Ganinta Tana Karanta Al Qur’ani Ba Dai Dai Ba. Yakamata A Kirata A Sake Mata Duka. Inda Daurawan Ya Bayyana Masa Cewa Ba Haka Akeyi Ba. Gyara Yakamata A Mata Na Karatun Domin Kusan Kowa Ma Yana Karantawa Ba Dai Dai Ba Sai A Masa Gyara.
Sheikh Daurawan Ya Bayyana Cewa Ita Nasiha Yakamata Ayi Mata Sannan Kuma A Mata Gyara Kan Abubuwan Da Takeyi A Nuna Mata Kuskurenta A Gyara Mata. Ko Da Zuwa Gaba Ta Gyara.
Ga Bidiyon Murjan Tana Karatun AlQur’ani Maigirma Ba Dai Dai Ba.
Ga Bidiyon Hirar Da Ayi Da Malam Aminu Ibrahim Daurawa.







