E News

Abba Gida-Gida Ya Naɗa Ganduje, Kwankwaso Da Shekarau Muƙami A Jihar Kano

Mai Girma Gwamnan Kano Abba Gida-Gida Ya Naɗa Ganduje, Kwankwaso Da Shekarau Muƙami A Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano domin ta zama mai ba da shawara ga gwamnatin jihar.

Gwamna Abba ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja.

‘Yan majalisar sun haɗa da tsofaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugabannin majalisar dattawa (Idan akwai), shugabannin majalisar wakilai, shuwagabannin majalisar dokokin jiha, mataimakan shugabannin majalisar, alkalan kotun ƙoli da suka yi ritaya, alkalan kotun ɗaukaka ƙara da suka yi ritaya, da tsofaffi manyan alƙalan jihar, tsofaffin sakatarorin gwamnatin jiha, da tsoffin shugabannin ma’aikatan jiha, waɗanda dukkansu ‘yan asalin jihar Kano ne.

Haka kuma majalisar ta haɗa da shugabannin Malamai, ‘yan kasuwa, sarakuna, tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano, da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da ayyana su.

Da wannan ne Rabi’u Musa Kwankwaso, Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Umar Ganduje suka zama mambobin majalisar.

Gwamnan ya jaddada ƙudirin sa na cigaba da gudanar da gwamnati a buɗe domin tafiya da kowa da kowa, a sabon yunƙuri na ganin Kano ta cigaba ta kowacce fuska.

Back to top button
error: Content is protected !!