Abba Gida Gida Ya Koka Kan Salon Aikin Hisbah
Hisbah Hukuma Ce Mai Albarka Wadda Muka Dauka Da Martaba, Kuma Muka Ɗauko Bayin Allah Wanda Muka San Za su Iya Muka Ce ga Amanar Al’ummar Jihar Kano. – Cewar Gwamnar Jihar Kano Abba Kabir Yusuf.
Amma ma’anar Hukuma shi ne ta yi abin da ya ke daidai kuma a bai wa Gwamnatin shawara sannan a samu hadin kai tsakanin Gwamnati da masu ruwa da tsaki.
Na ga wani bidiyo da ya tayar min da hankali, kira nake da jan hankali gyara muke so.
An ɗebi motoci, an je inda wasu matasa ke ɓarna maza da mata, amma yadda aka riƙa debo su ana duka da gora suna gudu ana bi, ana tadile kafafunsu, ana debo su kamar awaki haka a jefa su a cikin Hilux.
Wani ma Allah ya kiyaye in kashin bayansa ya karya Spinal Cord dinsa ya gama yawo har abada.
Wannan muna ganin kuskure ne babba, ka rungumo matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya a cikin Hilux.
Na ga bidiyo da aka je inda ɗalibai a Bayero suke har inda suke har dakunansu ana duka ana rungumosu, ana jefa su a cikin mota.
Mu muna ganin akwai gyara.
– Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf