Kannywood

A Shirye Nike Ga Duk Mai Son Ya Aure Ni:-Rahama Sadau

Wata tattaunawa da fitacciyar jarumar tayi da Mujallar Fim game da sabon wajen abincin da ta bude da kuma zancen lokacin da za ta yi aure. Ban da zancen lokacin aurenta, an tambayi jarumar game da alakarta da Sadiq Sani Sadiq da kuma fitaccen mawaki Akon.

Ga dai yadda hirar ta su ta kasance:

Dan Jarida: Me zaki ce game da wannan nasara da kika samu ta bude wajen sayar da abinci?

Rahama: Na fi kowa farin cikin bude wannan waje mai suna Sadauz Home, saboda na dade ina mafarkin bude wannan waje. Ganin yadda na bude wuraren kasuwanci masu suna Sadau da yawa, shine yasa nace bari na hade su waje daya, sai na ware shaguna-shaguna.

Dan Jarida: Menene gaskiyar maganar da ake cewa kina soyayya da Sadiq Sani Sadiq?

Rahama: E to, akwai soyayya ta ‘yan’uwantaka tsakani na da shi, amma ba wai soyayya irin wacce mutane suke tunani ba. Sadiq shine abokin da bani da kamar shi a masana’antar Kannywood, shine mutumin da tamu ta zo daya ta kowanne bangare.

Amma babu maganar soyyya tsakanina da shi, haka kuma hotunan da muka yi a baya na fim ne, kuma mutane sun ga fim din.

Dan Jarida: Shin kin yankewa kanki ranar da za ki bar harkar fim?

Rahama: Gaskiya ban yanke wani lokaci ba, ban ma tunanin barin harkar gabaki daya.

Dan Jarida: To ya zancen maganar aure?

Rahama: An kusa, da zarar miji ya zo!

Dan Jarida: Kina dai nufin Rahama Sadau har yanzu a kasuwa take?

Rahama: Gaskiya dai idan da mai so ya zo ya dauka!

Dan Jarida: A karshe mai zaki cewa masoyanki?

Rahama: Masoyana nagode da soyayya, sannan kuma a cigaba da hakuri da ni, nagode sosai.

Back to top button
error: Content is protected !!