Kannywood
A Matse Nake Da Nayi Aure – Jaruma Saima Muhammad
Ga duk wanda ya san harkar fina-finai ta Kannywood da dadewa, to ya san Saima Mohammed, fitacciyar ‘yar wasan fim, amma a shekarun baya-bayan nan jarumar ta bace bat.
A wannan hira ta musamman da BBC Hausa, Saima, wacce ‘yar asalin kasar Nijar ce, ta yi magana kan yunkurin da take yi na dawowa Kannywood, da dalilin da ya sa ta daina fitowa a dim da kuma dalilin da ya sa aurenta ya mutu.
Cikin dalilan da Saima ta fada na barin ta Kannywood har da cewa ta lura harkar fina-finan ba ta samun irin ci gaban da ya kamata duk da dadewar da aka yi, don haka ne ta janye jiki har sai abubuwa sun gyaru.
Jarumar ta kuma ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, “a matse nake sosai da son yin aure. Ina fatan Allah ya kawo min miji.