A Dawo Da Diezani Domin Biyawa Yan Kasa Hakkinsu
SHUGABA TINUBU YA GAGGAUTA DAWO DA DIEZANI NAJERIYA DON A KARBAWA ‘YAN KASA HAKKINSU DAGA GWAMNA DAUDA LAWAL – Anas Abdullahi Kaura
Wata gamayyar masu rajin kare jam’iyyar APC ta National Defence ta bukaci gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da kada ya kawo cikas ga kokarin da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ke yi na dawowa Najeriya ba tare da wasu kwararan dalilai na zargin aikata ba dai-dai ba.
Wannan ne a dai dai lokacin da ake ta cece-kuce a kan batun gudun hijirar da tsohuwar ministar ta yi kan tuhume-tuhume da dama da yaki da masu yiwa tattalin arziki ke yi mata.
Alison-Madueke yayin wata zantawa da manema labarai a birnin Landan, ta ce, an zargeta da laifin karkatar da kudi a lokacin da ta ke rike da mukamin ministar man fetur, inda ta ce kuma gaskiya ne, amma ta ce ta son Shugaba Bola Tinubu da ‘yan Najeriya su yafe mata, tare da bata damar dawowa Najeriya da nufin bayar da gudunmawar ciyar da kasar gaba, kasancewar komai na rayuwa wucewa yake.
Kungiyar ta yi zargin cewa tsohuwar ministar ta amince tare da danka amana ga gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, wanda ta ba wa sama da dala biliyan 9 don ya ajiye mata a lokacin da ya rike da mukamin Babban Darakta na First Bank Nigeria PLC.
Diezani ta shaida wa manema labarai cewa, mijinta da dukkan ’yan uwanta da lauyanta da ke zaune a Birtaniya sun san dangantakarta da Dauda Lawal Dare, Gwamnan Jihar Zamfara.
To sai dai rahotanni sun ambato Diezani na cewa abin takaici, yanzu Dauda Lawal ba ya daukar wayata, har ma yana hada kai da ‘yan sandan Burtaniya su sanya ido a kai na, inda ta yi zargin cewa mai yiwuwa yana kokarin mallakawa kansa kudaden da na ba shi a jiya, idan ba na raye
Da yake mayar da martani, kan al’amari shugaban gamayyar masu rajin kare jam’iyyar APC, Kwamred Abdullahi Anas Kaura, ya jaddada muhimmancin bin doka da oda, inda ya bukaci Dauda Lawal Dare da ya guji aikata wani abu da ake ganin zai kawo cikas ga kokarin wanzar da adalci.
Cikin wata sanarwar kungiyar ta ce Diezani Alison-Madueke, fitacciyar yar siyasa ce Najeriya, da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa a lokacin da take rike da mukamin ministar albarkatun man fetur.
Diezani Alison-Madueke ta musanta zarge-zargen sannan kuma ta bayyana cewa za ta koma gida Najeriya don warware duk tuhume-tuhume da aka yi mata.
Kwamared Kaura ya bukaci a tabbatar da adalci da kuma bin doka da oda, tare da bin dokokin kasa don wanzar da adalci da hakkokin ‘yan kasar, ta yadda za a kwato hakkinsu daga kowaye ba tare da la’akari da mukaminsa ba.
Coalition for National Defence ta ce yayin da ake ci gaba da wannan tirkatirka, al’ummar kasar sun sa ido sosai, tare da hankoran yadda za a warware wannan takaddamar da ke tattare da yiwuwar dawowar Diezani da kuma shari’ar da za ta iya biyo baya.
Bugu da kari, Kwamared Abdullahi Anas Kaura ya bukaci gwamna Dauda Lawal Dare da ya martabar al’ummar kasa da kuma kimarta a idon duniya. Sannan kuma ya jaddada muhimmancin bin ka’idojin shari’a tare da bai wa hukumomin da suka dace su binciki duk wani zargi da ake yi wa Diezani maimakon kokarin hana ta dawowa ba tare da wani dalili ba.
Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke kokarin karfafa tsarin dimokuradiyya da kuma tabbatar da adalci tare da tunatar da al’umma bukatar hadin kai wajen tunkarar al’amuran da suka shafi kishin kasa.
Kwamared Anas kaura ya roki masu kokarin tabbatar da adalci a harkokin shari’a kasancewar daukar kowanne dan kasa dai-dai da kowa a idon shari’a da doka.
Bugu-da-kari Kwamared Kaura yace ya yin da al’ummar kasar ke jiran yadda wannan babban al’amarin zai kasance a kotu, akwai bukatar abi doka da ka’idojin shari’a sau da kafa don tabbatar da adalci ga ‘yan kasa.